Kirkiro Ma’aikatar Kula Da Dabbobi: Miyyeti Allah Ta Jinjina Wa Shugaba Tinubu

IMG 20240317 WA0065

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta bayyana Godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa kafa ma’aikatar kula da dabbobi.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Baba Othman-Ngelzarma ya fitar a Yau Talata a Abuja, ya bayyana cewa kafa ma’aikatar zai samar da damar sana’ar kiwo a fadin ?asar.

Bugu da kari, ya bayyana cewa ma’aikatar ta kudiri aniyar samar da ingantattun guraben ayyukan yi masu inganci a duk fadin tsarin kimar dabbobi da nufin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Yace, “Da wannan ci gaban, MACBAN ta yi imanin cewa, fatan makiyayan Najeriya ya samu nasara a karkashin shirin sabunta fata.

“Alkawarin da shugaba Tinubu ya yi, na inganta ayyukan noma na Najeriya don tabbatar da samar da abinci yana cika.

“A madadin Shugaba da mambobin kwamitin amintattu na Kungiyar MACBAN, Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, da daukacin ‘ya’yan kungiyar Cattle Breeders ta Nijeriya a fadin ?asar nan suna taya shugaban kasa Kuma babban kwamandan kungiyar murna. Sojojin Najeriya don Samar da wannan gagarumin ci gaba.”

Related posts

Leave a Comment