Kiristoci Sun Yi Tir Da Ala?anta Ta’addanci Ga Pantami

Kwamitin hadin gwiwa kan kungiyoyin kiristoci da lamuran addini na Nijeriya, ya yi Allah wadai da zargin alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda da aka yi wa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami.

Shugaban kwamitin, Bishop John Okafor, ya bayyana matsayarsu a cikin wata sanarwa da ya fitar kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.

Wani bangaren, sanarwar na cewa: “Kwamitin bayan bincike ya gano cewa zarge-zargen da ake yi a kansa an yi su ne da nufin bata shi a matsayinsa na minista da kuma taba mutuncin kasar.

“Hakanan ta gano cewa Dr Pantami ta kowace fuska bashi da wata alaka ta sirri da kowane mai tsattsauran ra’ayi, a matsayinsa na Shehi da jami’in gwamnati.

“Binciken majalisar ya kuma gano cewa zarge-zargen sun kasance, zanga-zanga ce kawai ta masu ruwa da tsaki, wadanda sabon sauyi da aka samu a bangaren sadarwa ya shafa, karkashin kulawar Pantami.”

A cewar Bishop Okafor, Pantami Shehin addinin Islama ne, kamar yadda bishop-bishop da fastoci suke a cikin addinin kirista.

Ya kara da cewa ministan yana wa’azi ne kamar yadda aka koyar a cikin Alkur’ani mai girma, kamar yadda masu wa’azin kirista ke yi, a cewar Littafi Mai Tsarki.

Bishop Okafor ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su kasance masu adalci a cikin rahotanninsu da rahotanni game da masu yi wa gwamnati hidima.

Related posts

Leave a Comment