Kiristoci Sun Yaba Ƙoƙarin Da Nake Yi Wa Musulunci – Kabara

Shahararren mutum a jihar Kano wanda ake kira Abduljabbar Kabara ya bayyana cewa kiristoci sun fara yaba masa saboda kokarinsa wajen tsaftace addinin musulunci.

Abduljabbar Kabara wanda ke shan suka da caccaka daga bangarorin Malaman musulunci ya jaddada cewa aikin alkhairi yake yi wa addini wanda hakan zai amfanar da musulunci.

“Akwai kiristan da yayi waya da daya cikin masu daukan karatunmu, wani Faada, daga baya aka saka min hirar na saurara, wannan kirista ya bayyana cewa yana bibiyar karatukana, wannan kirista dan kwangila ne da ake daukar su su karanci musulunci don su yake shi, ya bayyana cewa a yadda yake da ilmin musulunci ba ya fargabar ya kara da kowanne Malami ko shehi amma ni ne kawai ba zai yi muqabala da ni ba ya kuma jinjina min bisa kokarin da nake yi wa musulunci” In ji Abduljabbar Kabara.

Haka nan Abduljabbar Kabara ya kara bayyana cewa bayan kiristoci an sami ‘yan kala kato wadanda suma suke yaba masa bisa ayyukan da yake na yaki da hadisan Annabi S.A.W.

“Nana Fadima A.S har korar ‘yan aikenta nake yi saboda yawansu, tana aiko min da sakon godiyarta bisa abin da nake yi.

Idan da mahaifina Malam Nasiru Kabara zai dawo duniya zai tafi ne akan abin da nake kai,
daga Barzahu ya aiko wani tsoho da ya zo wurina ya karbi Qadiriyya, wannan ke nuna lallai abin da nake yi daidai ne” Abduljabbar Kabara.

Wannan magana dai ta janyo cece-kuce da dama wanda ta kai an sami wadansu da ke fadin dama dole kiristoci su yabawa Abduljabbar Kabara saboda
kokarin rushe sunnar Annabi S.A.W sahabbansa uwa uba ma musulunci wanda wasu daga kiristoci suka sha alwashin dakile yaduwarsa.

Tun da jimawa ne aka sami malaman da ke zargin Abduljabbar Kabara da karbo kwangila daga makiya musulunci don rushe addinin, zargin da Abduljabbar Kabara ya musanta shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply