Kiran Fulani Da Sunan ‘Yan Ta’adda Na Iya Haifar Da Yaƙi – El Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi gargadi game da yiwa dukkan Fulani makiyaya kudin goro a matsayin masu laifi kuma masu kisan kai, ko kiran su ‘yan ta’adda kai tsaye, inda yace hakan ba ƙaramin kuskure ba ne da zai iya haifar da gagarumar matsala a Najeriya.

El-Rufai ya ayyana cewa aikata fashi da makami da sauran miyagun ayyukan na ta’addanci sun zama wata masana’anta kuma dole ne ‘yan Najeriya su hada kai don kawo karshen sa gaba ɗaya a ƙasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin shugabannin kungiyar Kiristoci ta Angilikan a Najeriya karkashin jagorancin Rebaran Henry Ndukuba a ziyarar da suka kai mishi fadar gwamnatin jihar.

Ya ƙara da cewar dukkanin ƙabilu da Allah ya halitta akwai masu kyau da marasa kyau a cikin su, yana mai bayyana ‘yan Najeriya bai kamata ba, saboda ayyukan wasu ‘yan kalilan masu aikata munanan ayyuka, su sanya sunan duk wani kabila ko wata kungiyar addini da ta’addanci ba.

“Akwai lokacin da fashi da makami ya kasance aiki ne na wasu keɓantattun mutane na wani yanki na ƙasar amma ba a taɓa bayyana su a matsayin ‘yan fashi da makami ne ba.
“Har ila yau, yaudara ta yanar gizo shima ya zama na musamman ga wasu yankuna na kasar amma ba a taba yiwa wata kabila lakani da Yahoo Boys ba.
“Wannan wani yanayi ne mai hatsari da zai iya kunna rikici a kasar nan. Akwai masu laifi daga cikinsu kuma dole ne mu gano su kuma mu magance su.”

Gwamna El Rufa’i ya kara da cewa: ‘’ Wannan rashin tsaro ya dabaibaye kasar nan. Kuma wasu ‘yan bata gari suna kokarin amfani da shi don kara raba mu ta hanyar kabilanci da addini.

“Ra’ayinmu a nan jihar Kaduna shi ne, a kowace kabila, a kowane addini akwai mutanen kirki da kuma mutanen banza. Kuma aikinmu a matsayinmu na shugabanni shi ne gano mutanen da ba su dace ba kuma mu kama su kuma mu gurfanar da su a gaban kotu.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply