Kimanin ‘Yan Jarida 50 Aka Kashe A Shekarar 2020 – Bincike

Akalla ‘yan jarida sama da 50 da suke bakin aiki aka kashe a shekarar 2020 mafiya yawansu a kasashen da ba su a cikin yake-yake.

Kididdigar ta bayyana mafi yawan yan jaridar da aka fi kai wa harin sun hada da masu bincike kan badakalar laifuka, cin hanci da rashawa da kuma sauran rigingimu.

Binciken ya bayyana kashe-kashen a Mexico, India da kuma Pakistan.

Kashi 84% na cikin wadanda aka kashe a wannan shekarar an farmakesu ne kai tsaye saboda aikinsu idan an gwada da kashi 63% na shekarar da ta gabata.

Babban editan jaridar RSF, Pauline Ades-Mavel ya bayyana cewa tsawon shekaru yan jarida masu binciken kwakkwafi na aikinsune akan tsini.

Related posts

Leave a Comment