Kimanin Matasa 2000 Ne Za Su Samu Aiki Ƙarƙashin Bizi Mobile

An ƙiyasta cewa kimanin Matasa 2000 ne zasu samu gajiyar aikin Banki da Kamfanin Bizi Mobile, kamfanin da ya saba hada hadar kuɗi ta zamani.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban Kamfanin Alhaji Aminu Bizi, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna.

Bizi ya bayyana cewar tuni kamfanin nashi bisa ga haɗin gwiwa da babban Bankin Najeriya,suka cimma wata matsaya na inganta rayuwar matasa da magance matsalar zaman banza, kuma kamfanin nashi ya bada fifiko sosai a yankin Arewacin Najeriya, kasancewar yankin na koma baya ta wannan bangare.

Hakazalika Kamfanin na Bizi ya shirya wasan ƙwallon kwando ga matasa domin kara jawo su jika, sannan Bankuna ne ake sa ran zasu ɗauki nauyin gasar, domin wadannan Matasa ne ake sa ran Kamfanin zai dauka aiki.

Matasan zasu dawo unguwanni da ƙauyukan su domin cigaba da buɗe asusun banki ga jama’a da samar da katin ATM ga jama’a, yadda jama’a musamman al’ummar Arewa zasu amfana sosai.

Labarai Makamanta