Ketare: Ukraine Ta Gargadi Iran Kan Goyon Bayan Rasha

Gwamnatin kasar Ukraine ta gargaɗi da kakkausan harshe ga ƙasar Iran da cewa ‘asarar’ da za ta tafka sakamakon goya wa Rasha baya a yaƙin da take a Ukraine ya fi ‘ribar’ da za ta samu na yin hakan.

Gargaɗin na zuwa ne bayan da a karon farko Iran ta amince cewa ta sayar wa da Rasha jirage marasa matuƙa, to sai dai tana mai cewa ta yi hakan ne tun kafin fara yaƙin Ukraine.

Ƙasashen yamma na zargin Rasha da amfani da jirage marasa matuƙa na Iran wajen kai hare-hare kan gine-gine masu mihimmanci a Ukraine, tare zargin cewa sojojin Iran na horas da dakarun Rasha kan yadda za su yi amfani da jiragen, zarge-zargen da Rasha da kuma Iran ɗin suka sha musantawa.

To sai dai a ranar Asabar ministan harkokin wajen ƙasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya shaida wa manema labarai a Tehran cewa ƙasarsa ta tura wasu jiragen marasa matuka da ba su da yawa zuwa Rasha, yana mai cewa sun yi hakan ne watanni kafin fara yaƙin Ukraine.

Labarai Makamanta

Leave a Reply