Ketare: Sojoji Sun Yi Ikirarin Kifar Da Gwamnatin Guinea

Rahotanni na cewa ba a san makomar shagaban kasar Guinea Alpha Conde ba, bayan wani hoton bidiyon da ba a kai ga tantance wa ba ya nuna sojoji na rike da shi, wadanda suka ce sun shirya juyin mulki.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa sojojin sun ce sun yi watsi da kundin tsarin mulkin kasar.

AFP kuma ya ruwaito cewa sojoji sun ce suna rike da shugaban kasar ya zuwa yanzu.

Tuni wasu jaridu musamman na kasashen da ke makwabtaka da Guinea ke ba da rahoton an yi juyin mulki a kasar.

Sai dai a gefe daya ministan tsaron kasar an ambato shi yana cewa an dakile yunkurin juyin mulkin.

Wannan na zuwa ne awannin bayan jin karar harbe harben bindiga a tsakiyar Conakry babban birnin kasar Guinea.

Labarai Makamanta

Leave a Reply