Ketare: Morocco Ta Halasta Noman Tabar Wiwi

A ranar Laraba ne hukumar kasar Morocco ta ba da izini 10 na farko don amfani da tabar wiwi a masana’antu, magunguna da kuma fitar da su zuwa kasashen waje.

Hukumar ta ce manoman da su ka kafa ƙungiyoyi a yankunan Al Houceima, Taounat da Chefchaouen ma su tsaunuka sannu a hankali za a ba su damar noman wiwi domin yin kasuwanci bisa matakin doka .

An riga an noma tabar wiwi a Marocco ba bisa ka’ida ba, kuma sabuwar dokar da majalisar dokokin kasar ta amince da ita a shekarar 2021, ba ta ba da izinin amfani da ita don nishaɗi ba.

An yi nufin dokar ne don inganta kuɗaɗen shiga na manoma da kuma kare su daga masu safarar muggan kwayoyi wadanda ke sarrafa cinikin tabar wiwi da fitar da ita ba bisa ka’ida ba zuwa Turai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply