Ketare: Matan Kasar Kenya Na Mutuwa A Saudiyya

Mata ‘yan ƙasar Kenya 85 da ke aiki a ƙasashen waje akasari Saudiyya ne suka mutu a cikin wata uku da suka gabata, kamar yadda wani ɗan siyasa ya faɗa wa majalisar dokokin kasar ta Kenya.

Gidan Talbijin na Citizen a kasar ya ambato Alfred Mutua, wanda a yanzu ake tantance shi a majalisar dokokin kasar domin nada shi a matsayin ministan harkokin kasashen waje ya kuma ce an tasa keyar wasu matan kasar kimanin 1000 zuwa kasar daga Saudiyyar.

Mafi yawan matan kasar Kenya kan tafi kasar Saudiyya da wasu kasashen yankin Gulf domin neman aiki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply