Ketare: An Kashe Shugaban Hamas Isma’il Haniyeh A Tehran

IMG 20240731 WA0033

Kungiyar Hamas ta ce an kashe shugaban ta Ismail Haniyeh a birnin Tehran na Iran.

Wata sanarwa da ?ungiyar ta fitar yau da safe ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Tehran, a ziyarar da yake domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.

?ungiyar falas?inawan mai ri?e da iko a Gaza ta ce Isra’ila ce ta kashe shugaban nata, Ismail Haniyeh, yayin da yake halartar rantsar da sabon shugaban Iran.

?ungiyar Hamas ta bayyana kisan a matsayin babban laifi wanda martanin sa ba zai zo da da?i ba.

Ta kuma ce Isra’ilan ta kashe ?aya daga cikin masu tsaron lafiyar Haniyeh, a lokacin samamen da ta kai.

Hamas ta kuma yi ta’aziyya ga Falasdinawa da Larabawa da kuma Musulman duniya da kuma a kan rashin jagoran nata.

Mafi yawan shugabannin ?ungiyar Hamas dai ba su fitowa fili su bayyana kansu, yayin da a gefe guda kuma, duk wa?anda suka bayyana kansun to za su gama rayuwar su ne suna wasan boyo da Isra’ila, mai neman rayuwar su ruwa a jallo.

Kafin wannan lokaci dai ana dai ganin Ismail Haniyeh a matsayin babban jagoran kungiyar Hamas, kuma yana cikin kungiyar tun daga 1980.

Ya ta?a zama firaiministan Falas?inawa na ?an?anin lokaci a 2006, amma daga baya aka sauke shi bayan Hamas ta ?wace mulkin Zirin Gaza daga hannun jam’iyyar Fatah.

A 2017 aka za?e shi shugaban ?angaren siyasa na kungiyar kuma bayan shekara ?aya Amurka ta sanya sunansa a cikin ?an ta’addan da ta ke nema ruwa a jallo.

Ya shafe shekaru yana zaune a Qatar.

Isra’ila ba ta fitar da sanarwa a game da wannan batun ba kawo yanzu, amma ministan al’adunta ya wallafa a shafinsa na X cewa ‘’kisan Haniyeh za ta tsaftace duniya’’

Hamas dai ta sha alwashin ?aukar fansa.

Related posts

Leave a Comment