Ketare: An Kashe Madugun ‘Yan Adawar Kasar Chadi

IMG 20240229 WA0299

Rahotannin dake shigo mana daga ƙasar Chadi na bayyana cewa wani mai shigar da kara na gwamnati ya ce an kashe wani madugun ‘yan adawa a ƙasar Chadi yayin wani artabu da jami’an tsaro.

Mutuwar Yaya Dillo na zuwa ne bayan da gwamnatin ƙasar ta zargi jam’iyyarsa ta adawa da kai wani mummunan hari da aka kai kan hukumar tsaron ƙasar, lamarin da Dillo ya musanta.

A ranar Laraba ne aka ji karar harbe-harbe a kusa da hedkwatar jam’iyyarsa da ke babban birnin kasar.

Mai gabatar da ƙara Oumar Mahamat Kedelaye ya tabbatar da mutuwar Dillo a ranar Alhamis.

Labarai Makamanta

Leave a Reply