Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya na bayyana cewar maƙasudin abinda ya haddasa mutuwar Basarakiyar Birtaniya, Sarauniya Elizabeth ta II ya bayyana.
A bayanan da ke ƙunshe a takardar shaidar mutuwarta, ya nuna cewa tsufa ne ya yi ajalin Sarauniyar wadda ta lashe shekaru 70 tana mulkin ƙasar ta Birtaniya.
A takardar shaidar da National Records of Scotland ta fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022, marigayya Sarauniya ta mutu ne da ƙarfe 3:10 na yamma ranar 8 ga watan Satumba, 2022 a Fadar Balmoral, Ballater. Musabbabin abinda ya haddasa mutuwar Sarauniya shi ne tsufa kamar yadda aka rubuta ɓaro-ɓaro a takardar kuma masarautar Ingila ta rattaɓa hannu.
Labarin mutuwar Sarauniya ya fito ne a wata sanarwa da Masarautar Ingila ta fitar a madadin iyalan Elizabeth ta II. “Sarauniya ta mutu cikin kwanciyar hankali a fadar Balmoral da yammacin nan. Sarki da Sarauniya za su zauna a Balmoral da yammaci kuma gobe za su koma Landan,” inji Sanarwan.
Elizabeth II ta kwashe shekara 70 a gadon sarauta Mutuwarta ya kawo karshen shekaru 70 da ta yi a karagar mulki, Basarakiya mafi daɗe wa a tarihin masarautar Ingila. Ta karɓi mulki ne bayan mutuwar mahaifinta Sarki George na IV a ranar 6 ga watan Fabrairu 1952.