Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu ta amince da nadin Sarakuna shida, a kananan Hukumomi shida dake fadin jihar.
Nadin ya hada da:-
1) Alhaji Muhammad Aliyu Maiyama, A Matsayin Sarkin Kudun Maiyama.
2) Alhaji Sadiq Ibrahim A Matsayin Sarkin Birnin Kebbi (Ubandoman Birnin Kebbi)
3) Alhaji Tukur Bahindi, A Matsayin Sarkin Bahindi
4)Yakubu Abubakar Kaoje, A Matsayin Sarkin Yamusa
5) Buhari Muhammad Aliero, A Matsayin Sarkin Aliero
6) Hamza Muhammad Na Gwandu, A Matsayin Sarkin Rafin Zuru.
Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kebbi, Hassan Muhammad Shalla ne ya bayyana hakan yau a Birnin Kebbi.
Kwamishinan ya taya Sarakunan murna tare da yi musu fatan alkairi.