Kawar Da SARS: Babu Dalilin Cigaba Da Zanga-zanga – Shugaban Majalisa

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ya ce zanga-zangar da ta barke a fadin kasar nan a kan cin zarafi da zaluncin da ‘yan sandan SARS ke yi, kwalliya ta biya kudin sabulu.

Bayan zanga-zangar a sassan kasar nan, Shugaban ‘Yan Sanda ya sanar da rushe runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami a ranar Lahadi, amma masu zanga-zangar sun ki barin tituna.

A yayin jawabi a zauren majalisar dattawa a ranar Talata, Lawan ya ce babu bukatar cigaba da zanga-zangar tunda an rusa rundunar. Shugaban majalisar dattawa ya ce a bai wa gwamnati damar hukunta tsohuwar rundunar da ake zargi da cin mutunci da zarafin jama’a tare da take musu hakki.

Shugaban ya ce, “Abinda jami’an SARS ke yi bai dace ba kuma ba za a lamunci hakan ba. Amma a tunani na kwalliya ta biya kudin sabulu kuma an samu abinda ake so.
“Babu bukatar a cigaba da zanga-zangar bayan an rushe rundunar kuma za a hukunta masu hannu a laifukan.

A tunani na ya kamata mu bai wa gwamnati damar tabbatar da abinda tayi ikirarin ta zartar. “Yan Najeriya suna da hakkin yin zanga-zanga. Gwamnati ta sauraresu kuma ta dauka mataki.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply