Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya gargadi shugabannin jam’iyyar APC da maaikacin da aka samu yana da hannu dumu-dumu a tallar wani dan takara a zaben 2023, za’a kore shi daga Jam’iyyar APC kwata-kwata, idan kuwa ma’aikacin gwamnati ne za’a dakatar da shi.
Masari ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da shugabanni jam’iyyar APC na jiha da kananan hukumomi talatin da hudu da kuma gundumomi dari uku da sittin daya a filin taron People’s Square da ke kallon gidan Gwamnatin Jihar Katsina a jiya Lahadi.
Gwamna Masari ya kara da cewa “wannan gwmnati da aka sake zabar mu, watan goma sha hudu da rantsar da ita. Shugabannin jam’iyya da sauran Jama’a, wallahi, wallahi, wallahi duk wanda aka kawo mani rohoto na gaskiya, yana yawon tallar wani dan takara kan 2023, tabbas zai bar mukaminsa idan yana rike da shi. Kuma tun daga ‘yan takarar majalisar jiha har zuwa Shugaban Kasa, saboda bai neman jihar alheri.
Masari ya kara da cewa idan wannan Gwamnatin ba ta yi abun alheri ba, to da wace jam’iyyar za ka nemi takarar. Duk wanda ku ka ga yanayin haka, ku gayaman domin daukar Kwakkwarar mataki a kansa na kora, idan ma’aikacin ne kuma za mu dakatar da shi.