Katsina: Za A Rabawa Tubabbun ‘Yan Bindiga Gidaje Da Shaguna

Gwamnatin jihar Katsina tana shirin gina rukunin gidaje da shaguna a kusa da wasu dazuka a jihar inda za a bawa tubabbun ‘yan bindigan su zauna domin inganta rayuwar su.

Gwamnatin jihar na sa ran gine rukunin gidaje a kusa da dazukan domin korar duk wasu ‘yan bindiga da ke buya a cikin dajin ya kuma bawa tubabbun yan bindigan damar fara sabuwar rayuwa.

Gwamnatin ta yi alkawarin bada gidaje, shaguna da filayen noma ga ‘yan bindigan da suka amince za su ajiye makamansu su mika kai ga jami’an tsaro.

Wani daga cikin shugabannin ‘yan bindiga mai suna Sada ya mika wuya ga sojojin na musamman na Fowarda Base da ke Dansadau. Ya mika bindigogi AK 47 guda uku da sub-machine gun da alburusai.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa ne ya sanar da shirin sassaucin da Gwamna Aminu Masari zai yi wa ‘yan bindigan da suka tuba yayin taron manema labarai a gidan gwamnati.

Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin ‘yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara, Inuwa ya kuma ce gwamnatin jihar kawo yanzu ta tallafawa hukumomin tsaro da Naira biliyan 4.274.

Ya ce gwamnatin jihar za ta gina gidajen ne a kusa da dajin Rugu, ‘Yantumaki, Maidabino da Sabuwa/Faskari.
A cewarsa, za a tanadi makarantu, cibiyoyin lafiya kasuwanni da filayen noma a rukunin gidajen da za a gina wa tubabbun ‘yan bindigan.

“Mun kammala shiri ga wadanda suka amince za su zauna a kusa da dajin Rugu, wannan na cikin tsarin da gwamnati ke yi na hana ‘yan bindiga zama a cikin dajin, kwamitin da aka kafa za ya fara aiki kowanne lokaci daga yanzu.

Labarai Makamanta