Katsina: Yara Bakwai Sun Mutu A Kokarin Tsere Wa ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar a ranar Alhamis ne wasu yara 7 suka rasa rayukansu a kauyen Shimfida dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina yayin gudun tsere wa harin ?an bindiga.

Mazauna kauyen Shimfida sun bayyana cewa wannan hari ya biyo bayan cire sojoji da aka yi ne a ?auyen.

Wani shugaban kungiya Adam Muntari TBO ya bayyana cewa karar bindigan da mutanen kauyen suka ji ya sa suka fara arcewa a tunaninsu ‘yan bindiga ne suka kawo musu hari.

Ya ce daga baya an gano cewa ‘yan bindigan na harbi a sama saboda suna murnan cire sojoji daga wata makaranta da aka yi ne.

Related posts

Leave a Comment