Katsina: ‘Yan Sanda Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Da Ceto Mutane Masu Yawa

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar tayi nasarar hallaka ‘yan Bindiga da dama tare da ceto dalibai 84 wadanda ‘yan bindigan suka sace a garin Mahuta da ke karamar hukumar Dandume a daren jiya.

Wannan ya biyo bayan kiran gaggawa da suka samu a ranar Asabar daga DPO na Dandume wanda ya sanar da cewa daliban Islamiyyar Hizburrahim guda 84 suna hannun ‘yan bindiga.

A takardar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya fitar a ranar lahadi, ya ce ‘yan sandan sun ceto daliban da ?arin wasu mutane hudu da kuma shanu 12 daga hannun ‘yan bindigan da suka nufi dajin Danbaure da niyyar barin garin da su.

‘Yan Bindiga a baya bayan nan sun tsananta kai hare hare a Jihar Katsina jihar da shugaban kasa Buhari ya fito, musanman tun a ranar farko da shugaban ya ayyana yin hutun mako guda a mahaifarshi wato birnin Daura.

Tashin farko ayarin wasu ‘yan Bindiga suka kaddamar da hari akan Makarantar Sakandaren Kimiyya da ke karamar hukumar ?an?ara inda suka yi awon gaba da ?aruruwan dalibai.

Sai gashi ba’a gama juyayin faruwar wancan ba wasu ‘yan Bindigar suka kara kai hari akan wata makarantar islamiyya da ke garin ?an Dume.

Related posts

Leave a Comment