Katsina: ‘Yan Sanda 30 Ke Gadin Ƙauyuka 100 – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya koka kan yadda ‘yan sanda gudan 30 ke kula da kauyuka guda dari a jihar Katsina.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi lokcin bikin Sallah da sojojin sama suka shirya a jihar.

Ya ce hakan ya sa suke tunanin samar da ‘yan sandan yankuna wadanda za su taimaka wajen kawo tsaro a jihar. Inda ya kara da cewa, muddin ba a dauki wannan mataki ba to ko da sojoji sun yi maganin ‘yan Bindigar wasu ‘yan ta’addan kan iya sake bulla Wasu wuraren.

Ya baiwa mutanen kauyukan shawarar su daina baiwa masu laifin mafaka saboda a rika samu ana gamawa da su ba tare da an kashe wanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Hukumar sojin ta sha alwashin samar da Jirgi marar matuki da zai yaki rashin tsaro a yankunan Katsinan da Arewa Maso Gabas.

Labarai Makamanta

Leave a Reply