Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Mata 17 Masu Goyo

Rahotanni daga yankin ?aramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina na bayyana cewar wasu ‘yan Bindiga ?auke da makamai sun yi awon gaba da wasu Mata 17 masu goyo cikin dokar daji.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar ‘yan Bindigar sun ?auke Matan ne a daidai lokacin da matan ke kan hanya zuwa bikin aure daga unguwar Rimi zuwa garin maigora.

Rahotanni sun bayyana cewar dukkanin matan 17 na ?auke da goyon jarirai a bayan su, kuma a hakan ‘yan Bindigar suka iza ?eyar su cikin kungurmin daji.

Yankin ?aramar Hukumar Faskari na ?aya daga cikin yanki dake fama da matsalar rashin tsaro a jihar, dalilin makwabtaka da yankin ya yi da kananan hukumomin Jahar Zamfara mai fama da rashin tsaro. Tare da cewar cikin garin Faskari da akwai sansanin sojoji da barikin ofishin ‘yan Sanda masu kwantar da tarzoma.

Related posts

Leave a Comment