Labarin da ke shigo mana da dumi-duminsa daga Jihar Katsina na bayyana cewa wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun yi awon gaba da dumbin dalibai daga wata makarantar sakandire ta kimiyya da fasaha da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
A ruwaito cewar ‘yan bindigar sun shiga har dakin kwanan daliban tare da yin awon gaba da su da duku-dukun safiyar yau, Asabar, bayan sun bindige masu gadin makarantar.
An bayyana cewa ana kidayar adadin daliban da ‘yan Bindigar suka sace, saboda daliban suna da tarin yawa, kuma ‘yan Bindigar sun tattara su gaba daya ne kafin suka arce dasu cikin dokar daji.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Nijeriya da ke fama da matsalar ‘yan bindiga. ‘Yan bindiga na cigaba da kai hare-hare a sassan jihar duk da yawan jami’an tsaro da aka tura da kuma atisaye daban-daban da suka kaddamar a yankin.
A baya, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya taba yin sulhu da ‘yan bindiga domin a samu zaman lafiya.Sai dai, sulhun bai yi wani tasiri ba, saboda ‘yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare tare da kisan mutane babu gaira, babu dalili, tare da yin awon gaba da dukiyoyinsu.
Bayan asarar rayuka da dukiyoyin al’umma, ‘yan bindiga na sace mutane tare da yin garkuwa da su domi neman kudin fansa. Wanna shine karo na farko da rahoto ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga makarantar kwana tare da yin awon gaba da dumbin dalibai a jihar Katsina.