‘Yan bindiga sun afka karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina inda suka yi garkuwa da surukar babban dan kasuwar nan Alhaji Dahiru Bara’u Mangal.
Majiya mai tushe daga iyalan Mangal wadda ta yi magana game da halin da ake ciki ta shaida cewa ‘yan ta’addan sun shiga garin ne da misalin karfe 1:00 na rana, inda kaitsaye suka tafi gidan surukar Alhaji Dahiru Mangal, Hajiya Rabi suka tafi da ita.
Majiyar ta kara da cewa ko a kwanaki ma masu garkuwar sun sace mahaifin matar dan ita Hajiya Rabi mai suna Buhari Muntari a cikin garin Katsina.
-Hausa7 Nig