Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Ango Da Amarya

Da misalin karfe tara na safiyar yau litinin, ‘yan bindiga suka tare hanyar kasuwar Gora, a dai-dai garin Gobirawa da ke Runka, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda Suka kashe wani dattijo, Malam Samaila Sufa, har lahira inda suka sassare shi kuma suka harbe shi sau biyu da kuma jima mutane hudu raunuka. Kuma a ranar asabar suka sace wata amarya da angonta, wanda satin su biyu da aure.

Majiyarmu da ba ta bukatar a bayyana sunan ta, ta shaida mana cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar zuwa kasuwar a dai dai kusa da garin Gora, inda suka hana, wucewa, da suka lura mutane sun ja birki, sai suka biyo akan mashina suna ta harbi, har suka iske Malam Samaila Sufa Runka, wanda sana’ar tukin motar haya ya ke. Har ila yau, kawu ne ga danmajalisar jihar Katsina, mai wakiltar karamar hukumar Safana, Abduljalal Haruna Runka. An yi janaizar sa da misalin karfe sha daya na rana a garin Runka, ya bar Mata daya da ‘yaya goma sha daya.

Haka zalika, ‘yan bindiga sun sace ango da amarya a garin Runka, da ke karamar hukumar Safana, a ranar asabar din da ta gabata, wanda a ranar ne suke cika kwana sha hudu da yin auren. Amaryar sunan ta Zainab da mijinta Ismaila, yanzu haka suna hannu yan bindiga.

Wata Majiyar ta shaida mana ko a jiya sun sace mutane goma sha biyu, a garin Babban Duhu, yau kuma sun tare hanyar zuwa kasuwar Gora har sau biyu kuma tsakanin su da shingen jami’an tsaro bai wuce kilomita daya ba. Da suka ga direbobin mota dauke da fasinjojin sun cirko-cirko a dai-dai garin Gobirawa, su ka biyo suna harbi mai-kan-uwa -da wabi, inda suka kashe mutum daya, hudu suka ji raunuka. Karamar Hukumar Safana na cikin kananan hukumomi jihar Katsina, da ke fama da matsalolin ‘yan bindiga.

Related posts

Leave a Comment