Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Faskari

Ƴan bindiga sun kai mummunan hari ƙauyen Shau a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina a ranar Lahadi inda suka kashe a ƙalla mutum takwas.

Mazauna garin sun ce ƴan bindigan sun ƙone gidaje masu yawa a kauyen sannan sun sace kayan abinci da wasu kayyakin biyan buƙatu. A

An ruwaito cewa ƴan bindigan har ila yau sun lalata motar dagajin ƙauyen, dalilin harin ya saka mutane da dama sun tsere zuwa ƙauyukan da ke makwabtaka da su.

Jami’an tsaro na haɗin gwiwa da suka amsa kirar mazauna ƙauyen sun yi bata kashi da ƴan bindigan sun kora su cikin daji.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo ya tabbatar da afkuwar harin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply