Kimanin sojoji 20 ne aka kashe a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka yi a jihar Katsina, a ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin da suka mutu a cikin Operation Sahel Sanity a Jibia, karamar hukumar Jibia ta jihar katsina, an kai musu hari ne a yayin da suka yi gaba zuwa sansanin shugaban ‘yan ta’addan jihar da aka fi sani da suna Dangote.
Wata majiyar soja ta ce jihar, Katsina dai tana fuskantarrhare-hare daga ‘yan bindinga wanda kawo yanzu ana hasashen cewa sama da mutane 300 a wannan shekarar kadai suka mutu wanda yawanci wadanda ‘yan Bindigar ne. suka halakasu.
A kwanakin baya shugaban dakarun sojin ƙasar Janar Buratai ya ziyarci jihar ta Katsina a matakin gani da ido, inda ya lashi takobin kawo ƙarshen ‘yan Bindigar.