Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban ‘Yan Banga

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a daren ranar Lahadi sun kashe shugaban kungiyar ‘yan sintiri a garin Maigora a karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina, Malam Ummaru Balli.

‘Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum takwas yayin harin da suka kai a kauyen Rimi da ke karamar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina.

An gano cewa Mallam Balli ya jagoranci wasu ‘yan sintiri zuwa Rimi domin su taka wa ‘yan bindigan da suka kai hari a Rimi birki a dare da abin ya faru amma Allah cikin ikonshi sai ya nufi jagoran ‘yan bangan da rasa ranshi a hannun ‘yan bindigan.

Mazauna garin sun bayyana cewa yan sintirin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan hakan ya yi sanadin rasuwar Mallam Balli. Yan bindigan daga bisani sun tsere sun tafi daji da mutum takwas da suka yi garkuwa da su.

Tuni dai an yi wa Mallam Balli jana’iza bisa koyarwar addinin musulunci. Kawo yanzu mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai riga ya yi tsokaci kan lamarin ba.
Kazalika, mai ba gwamna Aminu Masari shawara kan tsaro, Mallam Ibrahim Katsina bai daga wayarsa ba kuma bai turo da amsar sakon kar ta kwana da aka aike masa ba a lokacin wallafa wannan labarin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply