Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 15

Da misalin karfe tara na safiyar yau ne, ‘yan bindiga dauke da bindigogi bisa mashina suka kai hari a kauyen ‘Yar Gamji, dake karamar hukumar Batsari, inda suka kashe mutane goma Sha biyar har lahira, a cikin gonakinsu da safiyar yau, kuma ana neman mutune biyar da har zuwa marecen nan ba’a ga gawarsu ba.

A wata tattaunawa da RARIYA ta yi da Sarkin Ruma, Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, inda ya ce sun kai harin da misalin karfe tara na safiyar yau Litinin, yanzu haka da marecen yau akwai gawarwakin mutum Sha biyar a Babban Asibitin Garin Batsari. An kuma halbin mutum biyu daya na kwance asibitin Katsina daya Kuma na nan Batsari. Sannan akwai mutum biyar da ba’a gansu ba, an halbe su, sun je sun Fadi. Don me mutum zai zo gona. Gobe za’a yi masu zana’ida tara zuwa goma na safe anan garin Batsari.

Shima Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da kai wannan hari a kauyen Yar Gamji dake karamar hukumar Batsari inda ya ce tabbas sun kashe manoma goma sha biyar a gonakin su. Kuma tuni rundunar ta tura jami’an ta a yankin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply