Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Awon Gaba Da Mutane 17

Al’ummar garin Zakka a jihar Katsina sun ce wasu ‘yan bindiga da ba su san ko su waye ba sun kai masu hari inda suka sace mata 17 da kuma kwashe shanu da dukiyoyinsu.
Wani mazauni garin na Zakka da ke cikin ƙaramar hukumar Safana ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sun shiga garin ne tsakar daren Lahadi inda suka shafe sama da sa’a biyu suna fashi.

Ya ce ƴan bindigar sun shigo garin ne misalin karfe 12 na dare kuma suka f ara harbin bindiga wanda ya razana mutanen garin wasu suka ruga daji wasu kuma suka boye a cikin karan dawa da gero.
“Sun kwashe shanu da dama da tumaki sannan suka shiga gida gida suna kwatar dukiyar mutane kafin su tafi da mata da ‘yan mata 17,” inji shi.

Amma ya ce ɓarayin sun mayar da wata yarinya ƴar wata byar da haihuwa da kuma hudu daga cikin matan da suka ɗauka da ya ce suma Allah ya kuɓutar da su.
Ƴan bindigar dai ba su kashe kowa ba a garin na Zakka wanda a bara aka taba kai wa hari.

Babu dai wani bayani da ya fito daga jami’an tsaro game da harin.

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni daga wasu ƙauyuka na jihar irin su Batsari da Dutsinma da Jibiya da Faskari na cewa kaso mai yawa na manoman yankin ba su yi sharar gona ba a wannan shekara ballantana niyyar fara noma sakamakon matsi da suke fuskanta daga ‘yan bindiga.

Exit mobile version