‘Yan Bindiga a jihar Katsina sun kone kauyen Diskuru dake karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina kurmus, yayinda suka hallaka akalla mutane 20 a ƙauyen.
Daga cikin wadanda aka kashe akwai Maigari, jami’in Soja, mata da yara. An ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun dira kauyen ne da safiyar Alhamis, 29 ga Oktoba inda suka lalata gidaje akalla 60, suka kashe mutane, kuma sukayi awon gaba da wasu.
Daga cikin wadanda aka kashe akwai Maigari, Alhaji Sama’ila Hussaini; yaro dan shekara 12, Sanusi Sani, da kananan yara mata 2, Hanafiya Dauda da Asiya Maikara.
Sauran sune, Bishir Auwal (36), Anas Dan-yaya (29) Sule Dan-Yaya (27), Aminu Bala (40), Nura Abashe (36), Mai-‘Kaura Amadu (68), da Sa’idu Kurma Surajo (40).
Matan da suka rasa rayukansu sun hada da Zaytu Dan-yaya (36), Nana Sagiru (20), Abu Dauda (25) da Sahu Mai kara (20).
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Isah Gambo ya tabbatar da aukuwan lamarin amma yace mutane 12 aka kashe.
A cewar mazaunan gari, an samu nasaran ceto dukkan wadanda aka sace bayan tattaunawa da yan bindigan.