Tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara Ta Kasa, Mai Shariah Umaru Abdullahi (Walin Hausa) ya bayyana cewa sulhun da Gwamnatin Jihar Katsina, ta yi da ‘yan bindiga, da wani babban kuskure da barnar kudin talakkawa, saboda bai yi tasiri ba ko alama na kawo karshen kashe-kashen yan bindiga da suka addabi jihar Katsina.
Mai Shariah Umaru Abdullahi ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake tattaunawa ta musamman da manema Labarai a gidansa dake Katsina.
Tsohan Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Kasa, ya kara da cewa sulhun da aka yi da ‘yan bindigar, ba haka ya kamata a aiwatar da shi ba, saboda ya za’a ce dan taadda ya kawo bindiga a bashi dubu dari biyu da hamsin, da ya koma daji, sai ya sayi bindiga kirar Ak 47.
Walin Hausa ya cigaba da cewa duk duniya babu inda yaki ya haifar da nasara, kamata ya yi ayi sulhu da su, ta hanyar inganta rayuwar makiyaya, wato a samar masu da wurin kiwo da makarantu da ruwan sha da wajen kiwon lafiya. A da har Maaikatar kula da kiwon dabbobi ke akwai a lardin arewa, kuma duk shekara Gwamnati a kowane mataki tana kasafin kudi kan manoma kawai, amma su makiyaya ban da su, dole sai an zo an yi gyara da kuma adalci, sannan zaa samu zaman lafiya mai dorewa. Amma wannan yakin da ake yi ba zai haifawa kasar nan da Mai ido ba, saboda dukkan su yan kasar nan ne, sulhu shi ne hanyar da ta dace. Ayi shi kuma da kyakkyawar niyya, za a samu zaman lafiya.
Abun nan fa ba mu kadai ya shafa ba, nan gaba yayanmu da jikokin, ya za su rayu nan gaba, nan ne babbar matsala. A duniyar nan ba a taba yaki da bindiga wanda aka karasa shi da bindiga da bindiga ba, bisa teburi ake sulhunta shi. Masana tsaro suna cewa baa sulhunta wa da yan taadda, wannan gurguwa shawara ce, saboda ko Amerika da ke cewa ba ta sulhu da yan taadda, ai su yan taadda na su ba yan kasar Amerika ba ne, mutane wata kasa ne suke kai masu farmaki. Mu kuma yan bindigar nan yan kasar nan ne, sai ace ba za’a yi sulhu da su ba.