Katsina: Ruwan Sama Na Kawo Mana Tsaiko Wajen Yaƙi Da ‘Yan Bindiga -Masari

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, a ranar Laraba ya ce ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya na daya daga cikin kalubalen da hukumomin tsaron da ke yaki da ‘yan bindiga a yankin arewa ke fuskanta.

Masari ya kuma bayyana fargabar cewa rashin zaman lafiyan da ake fama da ita a sassan kasar nan na iya barazana ga samar da abinci a kasar.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin zantawarsa da manema labarai a gidan gwamnati bayan taron da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa ta Aso Rock Villa a Abuja.

Masari ya ce jamian tsaron suna fuskantar kallubale wurin zirga zirga na motocin yaki na sojoji a lokacin damina saboda laushin kasar da ke dajin da yan bindigan suke fakewa.

Amma duk da hakan ya bayyana gamsuwarsa cewa za a magance kallubalen kuma za a samu nasara a kansu.

Gwamnan ya ce, “Akwai daji masu girma da hanyoyi masu wahalar bi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya inda yan bindigan ke buya.

Yanzu lokacin damina mu ke, akwai wahalar tafiya da manyan motocin yaki na sojoji domin kasar laushi gare ta kuma ruwan sama ya yi yawa. Amma dai za a cimma buri. Babu abinda ba zai yi wu ba idan har akwai niyya kuma an dage.

Masari ya ce a halin yanzu akwai sojoji kimanin 2,000 a Katsina inda za su yi taron su na shekara wadda hakan alama ce da ke nuna wa yan bindigan cewa sojojin sun shirya tsaf don yin maganinsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply