Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda Sanusi Buba, sun yi nasarar cafke wani hatsabibin mai garkuwa da mutane da fashi da makami, tare da hadin gwiwa da ‘yan banga, Abdullahi Ibrahim, wanda aka fi sani da Danda, dan shekara talatin da biyar da haihuwa dake garin Malabo a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyanawa manema labarai, inda ya ce ya dade yana addabar kananan hukumomi Batsari da Safana.
A cikin binciken an samu bindiga kirar Ak47 da shanun sata guda bakwai a hannun sa. Kuma ana ci gaba da bincike.
Jihar Katsina dai na cigaba da fuskantar barazana ta ‘yan Bindiga da masu garkuwa da mutane, a wani rahoton da aka fitar a kwanan nan na nuna cewar sama da ƙauyuka takwas a yankin ƙaramar Hukumar Faskari.