Katsina: Na Ci Duka Kamar Jaki A Hannun ‘Yan Bindiga Bayan Gano Ni Soja Ne

Wani Soja, mai mukamin Saje da ke aiki a Maiduguri, da ya zo ganin gida da kuma jinyar raunin da ya samu a kugun sa, ya bayyana yadda yan bindiga suka sace shi da yadda suka kuntata ma shi a lokacin da ya ke hannun su na tsawon kwanaki ashirin da shidda.

Sojan ya ci gaba da cewa daga Maiduguri na taho domin yin jinyar raunin da na samu, sun tsaya a wani daji na wajen Gurbin Baure, na take suka fara barin wuta, har suka fashe mani tayoyi, suka jefa ni wani rami, inda muka tafi dajin a kasa.

Da ya ke bayyana irin rayuwar da muka a daji ban sa ran zan fito ba, sai dai na yi hamdala ga ubangiji, na dauka jarrabawa ce ta ubangiji. Kullum sai sun buge ni da bulala kuma ido na a rufe yake da wani kyalle ban ganin haske. Abinci kuma sau biyu suke ba mu.

Sajen ya kara da cewa bayan sun sace ni da iyalina, sun nemi a ba su miliyan daya da rabi domin sako iyalina, wadda tun aka ba su kudin, kuma sake su, bayan amsar kudin fansar, Amma suka ci gaba da tsare ni, har tsawon wadannan kwanakin har yau kuma da aka kubutar da mu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply