Katsina: Muna Neman Ɗalibai 330 A Hannun ‘Yan Bindiga – Masari

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa akalla dalibai dari ukku da talatin da ukku, ke hannu yan bindiga da suka shiga makarantar sakandire ta Kimiyya ta maza da ke garin Kankara a jihar Katsina, suka sace.

Masari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke karbar babbar tawagar manyan jami’an tsaro, na gwamnati tarayya karkashin jagorancin Mai baiwa Shugaban Kasa shawara ta fuskar tsaro, Janar Babagana Mungono, da suka kawo ziyarar jajentawa iyaye da malaman makarantar da al’ummar jihar Katsina da kuma gwamnatin jihar Katsina a yau lahadi.

Makarantar Sakandire ta Kimiyya da ke garin Kankara tana da yawan dalibai dari takwas da talatin da Tara ne, masu kwana, yan sanda jihar Katsina sun ce lokacin da aka kawo harin wasu sun haura ta katangar makarantar sun dire, kuma ana cigaba da kokarin kubutar da su.

Cikin manyan jami’an tsaro da suka kawo ziyarar sun hada da Shugaban sojojin kasa, Tukur Yusuf Buratai da Ministan Tsaro, Alhaji Bashir Magashi da Shugaban DSS Da NIA Alhaji Rufa’i Ahmed.

Har yanzu ana ci gaba da tantance adadin yawan daliban da suka samu kubucewa da kuma wadanda ‘yan bindiga suka save a makarantar kwana ta Kimiyya ta karamar hukumar Kankara, da ke jihar Katsina, da yan bindiga suka sace a daren juma’a. Sakamakon hakan gwamnati jihar Katsina, ta rufe illahirin makarantun sakandire da firamare a jihar Katsina.

Labarai Makamanta

Leave a Reply