Katsina: Mun Kashe Biliyan Huɗu Da Dubu 200 Wajen Yaƙi Da ‘Yan Bindiga – Inuwa

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, kuma Shugaban kwamitin tsaro na jihar Katsina, Alhaji Mustapha Mohammad Inuwa, ya bayyana cewa daga 2015 zuwa Watan Augusta na wannan shekarar, Gwamnatin Jihar Katsina ta kashe zunzurutun kudi har naira biliyan hudu da miliyan dari hudu, domin tallafawa jamian tsaro masu aikin yakar wadannan yan bindiga da suka addabi wasu kananan hukumomi Jihar Katsina.

Mustapha Inuwa ya bayyana haka ne lokacin da zantawa da manema Labarai akan nasarorin da Gwamnatin Jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta samu a fannin tsaro.

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, ya ci gaba da cewa a kokarin Gwamnatin Jihar Katsina domin ganin an samu zaman lafiya, da Kuma karawa jamian tsaro kaimi da kwarin gwiwa muka kashe wadannan kudade. Har ila yau mun ba wasu jamian masabki da kuma gyara masu wasu daga cikin matsugunni na su. Kuma muna bada tallafi ga wasu daga cikin shirye-shiryen jami’an tsaro daban daban, domin dakile hare-haren yan bindigar kamar su Operation Sharar Daji da Operation Puff-Adder da Operation Mesa da Operation Dirar Mikiya da Kuma Operation Sahel Clean. Sakamakon wannan yunkuri na Gwamnatin Jihar Katsina na tallafi ga jamian tsaro, ya haifar da da Mai ido, kusan ana samun sauki kai hare-haren yan bindigar a halin yanzu.

Dakta Mustapha Inuwa ya kara da cewa an amshi bindigu, sama da dari bakwai daga hannun tubabbun yan bindiga, haka kuma an hannanta shanu sama da dubu ukku a hannu masu su na ainahi, wanda yan bindigar suka sata.

Labarai Makamanta