Katsina: Masari Ya Sallami Shugaban Jami’ar Umaru Yar’adua

Labarin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar Majalisar Zartaswa Jihar Wadda Gwamna Aminu Bello Masari ke Jagoranta ta Amince da Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina Farfesa Sanusi Mamman ya gaggauta Ajiye muƙaminsa,

Sauke shi daga muƙamin ya biyo bayan Rahotan da Gwamna ya kafa ne ya ba shi shawara, kan Rahotan da aka gabatar mashi akan Korafe-korafe da aka gabatar akansa.

Mai baiwa Gwamna Shawara kan Ilimi mai Zurfi, Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da maanema labarai, Jim kaɗan da fitowarsu daga zaman Majalisar Zartaswa a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina ranar Laraba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply