Majalisar zartaswa ta jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kafa wani kwamiti na musamman, domin zakulo yawan marayun da suka rasa iyayen su da kuma zawarawa da suka rasa mazajen su, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a kananan hukumomi goma sha daya da suke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina.
Kwamishinan yada labarai na jihar Katsina da harkokin cikin gida, Alhaji Abdulkarim Yahaya Sirika ya bayyanawa manema labarai hakan, bayan kammala zaman majalisar zartaswa da gwamna Masari ya jagoranta a jiya laraba.
Abdulkarim Yahaya Sirika ya kara da cewa an zabo mutane ashirin, wanda aka zabo daga fannoni daban-daban, wanda mataimakin gwamna, Alhaji Mannir Yakubu zai jagoranta. Aikin kwamitin shi ne ya gano hakikanin yawan zawarawa da marayun da suka rasa iyayensu, domin duba yadda gwamnati za ta taimaka masu.
Kananan hukumomi da ke fama da wannan matsalar ta rashin tsaron sun hada Batsari da Dutsinma da Faskari da Sabuwa da Dandume da Safana da Jibia da Danmusa da Kankara da kuma Kurfi.