Sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a makarantar Kimiyya ta maza da ke karamar hukumar Kankara, inda suka yi awan gaba da dalibai da dama, wanda har zuwa yanzu ba a san adadin su ba. Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe illahirin makarantun kwana na jihar Katsina.
Gwamna Aminu Bello Masari ya bada umurnin ne, lokacin da ya kai ziyara gaggawa a makarantar Kimiyya ta Kankara da safiyar yau, domin gane ma kanshi halin da dalibai suke ciki da kuma daukar matakan da gwamnatin jihar Katsina za ta dauka.
Masari ya nuna kaduwarsa da wannan ta’addanci na satar daliban, inda ya baiwa iyayen yara hakuri kuma gwamnatin jihar da tarayya za su yi bakin kokarin su, na ganin an kubutar da su cikin koshin lafiya. Yanzu haka jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojojin sama da kasa da kuma jami’an tsaro na farin kaya, sun shiga dajin domin ganin an kubutar da su.
Shima ana shi jawabi, kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce zuwa yanzu an ceto yara sama da dari biyu, sakamakon kokarin da baturen yan sanda ya yi da jami’an yan sanda.