Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnatin Jihar Karkashin Gwamna Aminu Masari ta umarci makarantun kwana a jihar Katsina da su sake budewa a ranar Talata, 2 ga watan Maris.
Kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Charanchi ne ya sanar da haka ga manema labarai dake fadar gwamnatin jihar a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu.
Da yake karin haske game da umarnin bayan ganawarsa da manyan jami’ai a ma’aikatar sa, Charanchi ya ce daliban makarantun kwana na sojoji guda hudu da ke jihar za su koma karatu gadan-gadan.
Makarantun sun hada da ta sakandaren sojoji na gwamnati, Faskari; makarantar sakandaren sojoji na gwamnati ta Musawa; sakandaren sojoji na gwamnati ta ‘yan Mata, Barkiya, da makarantar sakandaren’ yan sanda, Mani.
Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa ?alibai maza a sauran makarantu su je makarantar sakandare mafi kusa da wuraren zamansu yayin da takwarorinsu mata za su jira jin mataki na gaba.
Iyaye a Jihar Katsina sun shiga cikin zullumi da tashin hankali tun bayan farmakin da Fulani ‘yan Bindiga suka kai akan ?aliban Makarantar Sakandaren Gwamnati dake garin ?an?ara.