Katsina: Masari Ya Bada Umarnin Bu?e Makarantun Kwana

Rahotonnin dake shigo mana yanzu daga jihar Katsina na bayyana cewar gwamnatin Jihar ?ar?ashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta bada umarnin sake bude makarantun Kwana dake fa?in Jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Charanchi ne ya sanar da haka ga manema labarai dake fadar gwamnatin jihar a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu.

Da yake karin haske game da umarnin bayan ganawarsa da manyan jami’ai a ma’aikatar sa, Charanchi ya ce daliban makarantun kwana na sojoji guda hudu da ke jihar za su koma karatu gadan-gadan.

Makarantun sun hada da ta sakandaren sojoji na gwamnati, Faskari; makarantar sakandaren sojoji na gwamnati ta Musawa; sakandaren sojoji na gwamnati ta ‘yan Mata, Barkiya, da makarantar sakandaren’ yan sanda, Mani.

Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa ?alibai maza a sauran makarantu su je makarantar sakandare mafi kusa da wuraren zamansu yayin da takwarorinsu mata za su jira jin mataki na gaba.

Iyaye a Jihar Katsina sun shiga cikin zullumi da tashin hankali tun bayan farmakin da Fulani ‘yan Bindiga suka kai akan ?aliban Makarantar Sakandaren Gwamnati dake garin ?an?ara.

Related posts

Leave a Comment