Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana takaicinsa ga wasu daga cikin malamai, idan suna hudubar kafin liman ya zo, suna amfani da wannan damar ta ba da labarin da mafi yawancin sa, ba su da hujja ko sani ko tabbacin akan sa, amma su zo gaban mumbari suna fada.
Aminu Bello Masari ya bayyana haka ne, a wajen taron karawa juna sani na wuni daya, Mai taken “Inganta Tsaro A Cikin Jihar Katsina Tare Da Guddumuwar ‘Yan Jarida” da ofishin Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro ya shiryawa manema labarai da jami’an hulda da jama’a na kananan hukumomi da kuma masu mu’amala da shafukan sadarwa tare da hadin gwiwa da kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Katsina ta shirya a dakin taro na hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomin da ke hanyar Kaita, cikin garin Katsina.
Gwamna Masari ya ci gaba da cewa na so ace kun kira malaman addinin, domin suma suna da gagarumar guddumuwar da suke badawa a harkar tsaro, kuma da yawan su, sun dauka mumbarin, wata hujja ce ta bada labarai da ba su da ilimi akan shi. Malami zai zo yana fadin abu akan shugaba ba tare da an yi mai uzuri ba ko ji yadda hakikanin abu yake, misalin mun ji abu kaza, minene gaskiyar abun ta hanyar tuntuba. Kawai ta jin jita-jitar sai ya hau ya zauna, shi ne hujjar sa. Allah ubangiji duk ya san duk wani abu da dan Adam ke aikatawa a doran kasa, amma duk da haka, idan ya je lahira sai an yi masa hisabi a gobe kiyama.
Masari ya kara da cewa, akwai hanyoyi da dama da za’a bi ayi wa shugabanni wa’azi, ciki tattausan harshe, yadda za’a samu kyakkyawar fahimta, inda gyara yake, a gyara. Amma wasu na yi da gangan ko wulakanci, hikimar isar da sakon ba ta zo ba, kuma ba ta yi aiki ba, saboda hanyar da aka bi aka isar da sakon. Ka ji malami ya zo ya ce yana da mabiya a shafinsa na dandalin sada zumunci na fesbuk dubu ashirin, ya za’a yi wannan ya zama wani ma’auni ne ko hujja ta ka zo ka zagi shugabanni? Akwai kasashen musulmi da dama, kuma suna bin hanyar idan shugabanni sun kauce ana jawo su, amma cikin hikima.
Da ya juya wajen masu rubuta labarai, musamman wadanda ke rubuta labarai na karya ko kanzon-kurege da su sani cewa, za su yi bayani ranar gobe kiyama. Duk abinda aka rubuta ba ana yi bane don shugabanni su karanta ko dan yin gyara,suna yi ne don duniya ta gani. Zaman lafiya ba na shugabanni ba ne kadai, na kowa da kowa ne.
Shima da yake jawabi, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina, mai baiwa gwamna shawara a harkokin tsaro, ya ce taron zai taimaka wajen inganta tsaro a jihar Katsina.