Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Katsina: Majigiri Ya Sake Ɗarewa Shugancin PDP

A ranar litinin ne, jam’iyyar adawa ta PDP ta shirya zaben shugabannin jam’iyyar a matakin jiha, wanda za su jagorancin jam’iyyar u, inda wakilai sama da dubu ukku da dari bakwai, suka jefa kuri’u daga gundomomi dari ukku da sittin da daya daga kananan hukumomi talatin da hudu, inda suka kara zabar Shugaban jam’iyyar Alhaji Salisu Yusuf Majigiri a matsayin Shugaban jam’iyyar na jihar Katsina a karo na biyu.

Zaben ya gudana ne a helkwatar jam’iyyar PDP da ke kan hanyar Katsina zuwa Kano, wanda ya samu halattar dan takarar Gwamna a zaben da ya gabata na 2019, Sanata Yakubu Lado Danmarke da wasu jiga jigan jam’iyyar. Zaben ya gudana a karkashin jagorancin Wakilan da uwar jam’iyyar PDP ta turo daga Abuja karkashin jagorancin Chika Nwazuzo da kuma sa idon wakilan hukumar Zaben Mai Zaman Kanta Ta Kasa reshen jihar Katsina.

Da yake bayyana wanda ya yi nasarar zaben Shugaban Kwamitin Zaben, Wanda Uwar jam’iyyar ta turo Mista Chika Nwazuzo ya ce kimanin kujeru talatin da tara ne, aka gudanar da zaben su a yau. Jimlar wakilan da suka jefa kuri’u dubu ukku da dari bakwai da goma sha takwas ne, an tantance jimlar dubu ukku da dari shidda da daya, an samu kuri’un da suka lalace hamsin da daya. Zababben Shugaban jam’iyyar, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya samu kuri’u dubu ukku da dari biyar da bakwai. Don haka ya zama sabon Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Shima da yake jawabi, Shugaban jam’iyyar da aka sake zabar, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana godiyarsa ga Wakilan jam’iyyar PDP tun daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi talatin da hudu na jihar Katsina. Haka kuma yau jam’iyyar PDP ta kammala, domin an samu zababbun shugabannin a kowane mataki a jihar Katsina.

Majigiri ya kara da cewa jam’iyyar PDP ita ce mafitar yan jihar Katsina dama Nijeriya gaba Daya. Kuma ita za ta ci zaben Gwamna da sanatoci ukku na jihar Katsina da yan Majalisar Tarayya sha biyar da kuma yan Majalisar Jiha talatin da hudu a 2023 da yardar Allah. Domin kawo karshen hare-haren yan bindiga, sun kashe kiwon lafiya. Jam’iyyar PDP za ta dawo ta bada mulkin adalci da walwala.

Da yake na shi jawabin, dan takarar Gwamna, a zaben da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Danmarke ya bayyana godiyarsa ga Wakilan jam’iyyar PDP da suka gudanar da zaben, kuma an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali ba tare da wata hatsaniya ba. Kuma wannan tafiya tana tare da nasara da adalci. Ina taya murnar wadanda aka zaba a matakai dabab daban, Allah ya taya ki riko. Muna mika godiyar ga shugabannin kwamitin wannan zaben.

Exit mobile version