Rahotannin da ke shigowa jaridar Muryar ‘yanci daga majiya mai karfi sun tabbatar da cewa Mai Garin Radda cikin karamar hukumar Charanci jihar Katsina da ‘yan bindiga suka sace a makon jiya ya kubuta.
”Ahmad Mande wani dan aslain garin na Radda ya shaida mana cewar Mai Garin Alhaji Kabir Umar ya samu kubuta da daren jiya talata wayewar garin yau Laraba inda aka garzaya dashi wani asibiti dake jihar Kano domin duba lafiyarsa.
”Sai dai har yanzu babu takamaiman bayanin ko kudin fansa aka biya kafin a sako shi ko kuma tserewa ya yi daga hannunsu.
”Kwanaki 4 dai Mai Garin ya kwashe a hannun wadanda suka sace shi, bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a garin na Radda a ranar 22 ga wannan wata na Janairu.
”Ko bayan sace shi da kwana daya, sai da iyalansa suka yi waya dashi yace yana cikin koshin lafiya a dajin Zamfara.