Katsina: Likitoci 30 Za Su Bar Jihar Dalilin Rashin Biyan Albashi

Ƙungiyar sabbin likitocin (Medical Doctors) da jihar Katsina ta dauka yan asalin jihar sun nuna takaicinsu matuka a kan yadda gwamnatin ke masu rikon sakainar kashi na rashin basu hakkonsu na alawsu-alawsu sama da watanni shida da suka gabata.

Katsina Daily Post News ta rawaito mana cewa wata wasika da suka fitar da sabbin likitoci 22 wadanda ke aiki a manyan Asibitocin dake fadin jihar Katsina suka rattaba ma hannu sun ce hakkokan nasu da suka hada da, gyaran albashi, da biyan su kudadden duti, da kudaden kira da dai sauransu, da suka makale ba a biya ba tun suna cikin yi wa kasa hidima har suka zo suka kama aiki da gwamnatin jihar Katsina bisa alkawari, ga shi yanzun tun wasunsu ba su da iyali yanzun sun yi aure nauyi ya fara hawa kansu, amma gwamnati ta yi nauyin hannu wajen biyansu hakkokinsu kamar yadda ake biyan sauran likitoci

A sanarwar likitocin sun bayyana cewa sun so danne abin dake damunsu na rashin biyan kudaden nasu, amma ta kawo masu iya wuya ne, shi ya sa har suka yi kira a kafafen sadarwa domin Gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki game da hakan.

A zantakwar da majiyar tanu ta yi da daya daga cikin sabbin likitocin game da lamarin, ya tabbatar mana da cewa matsalar ba daga wajen gwamna take ba, domin ” Gwamna ya bayar da umurnin a biya mu tuntuni, sai dai abin tun da ya je ofishin akanta janar na jihar Katsina komai ya tsaya cak ba amo ba labari, don haka muna kai kukanmu ga mai girma gwamnan jihar Katsina da duk wasu masu ruwa da tsaki akan abin da ya shafi lamuran kiwon Lafiya na jihar Katsina da su san halin da muke ciki ” inji daya daga cikin likitocin da Katsina Daily Post News ya zanta da shi game da lamarin.

Ya kuma kara tabbatar mana da cewa duk yadda suke son taimakon jihar Katsina, idan suma babu abin da za su iya tsare mutuncin kansu da na iyalansu to dole ne su samar wa kansu mafita

Labarai Makamanta

Leave a Reply