A cikin daren jiya ne da misalin ?arfe ?aya na dare (01:00Am) jami’an kwastam suka shiga cikin kamfanin Alfijir Bread, inda suka kwashe musu buhunnan shinkafar da su ke rabawa al’ummah, a cikin watan Ramadan mai girma a duk shekara.
Kamar yadda Gidauniya Tv ta ruwaito, ta samu zantawa da shugaban ma’aikan kamfanin Alfijir Bread Abubakar Nashala, inda yake cewa “na yi mamakin yadda aka kwashe mana buhunnan shinkafa guda 51 da zamu rabawa bayin Allah, a cikin watan ramadan mai daraja, kuma shinkafar siyota mukai a cikin ?asar nan ba daga ?asar waje muka siyo ba, kuma duk shekara mike rabawa gajiyayyu, da ?ananun ma’aikata ba siyarwa mike ba”.
Wani ma?wabcin Alfijir Bread Malam Salisu ya koka, inda yake cewa “mu talakawa muna amfana da sadakar da kamfanin Alfijir Bread yake raba mana a dai dai lokacin da ake fara Azumi, sai dai wannan shekarar jami’an kwastam sun zo sun kwashe abincin da za a ba mu, ni da naji ?arar motarsu zansa ?arayi ne bayan na le?o ta katanga ta, sai da safe aka ce min jami’an kwastam ne”.
Mun yi ?o?arin zantawa da manajan kamfanin, amma bamu samu damar hakan ba, mun kira shi domin muji ta bakinshi, amma bai ?auka ba har muka bar kamfanin.