Katsina: Kujerar Ɗan Majalisa Na Rawa Dalilin Aibanta Buhari

Jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Mashi ta umarci dan majalisar dake wakiltar Mashi da Dutsi, Mansur Mashi, ya janye kalaman batancin da yayi kan shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma jam’iyyar da mutanen da yake wakilta su fara shiran yi masa kiranye.

Shugaban jam’iyyar, Armaya’u Doka ya soki wadannan kalamai inda ya ke cewa hakan ci wa jam’iyyar mutunci ne a idon mutane da ‘yan adawa.

An samu wani rikodin da aka yi a asirce dan majalisa Mashi na ragargazar shugaba Muhammadu Buhari, da jam’iyyar APC.

A cikin kalaman da ake zargin Mashi yayi sun hada da alakanta jam’iyyar APC da filin kwallon kafar da ruwa ya kare mata, cewa ba za ta samu goyon bayan mutane ba a 2023 sannan shugaba Buhari, ba shugaba bane da zai iya mulkin Najeriya.

Bayan haka dan majalisar tarayyar ya bayyana cewa muddun dai ana son a samu ci gaba a Najeriya sai dai fa idan abinda ya samu marigayi Umaru ‘Yar’ adua, wanda ya rasu yana mulki, mataimakin sa ya dare shugabancin Najeriya, ya afka wa Buhari, shima, Yemi Osinbajo ya dare mulki.

” Dan majalisar ya shaida cewa dole sai abinda da ya afka wa marigayi Umaru ‘Yar’adua ya dirawwa Buhari, Osinbajo ya dare kujerar mulki kafin asamu cigaba a Najeriya.”

Sannan kuma ya kara da cewa, duk da dan majalisar Mashi na cin moriyar zabar sa da ‘yan mazabar sa suka yi, ya koma ya na caccakar su inda yake cewa dukkan su dakikai, jahilai gidadawa ne.

Ina so in sanar muku cewa kowa ya je ya saurari wannan rikodin, tana nan tana yawo a gari. Amma ina so in sanar masa cewa ta Allah ba tashi, APC za ta yi nasara a 2023.

” Muna kira ga jam’iyya a Jiha da Kasa baki da ya ta hukunta shi bisa wadannan kalamai sannan, majalisar kasa ta dakatar dashi. Idan kuma ba haka ba mu a yankin da yake wakilta za mu yi abinda ya dace.

Mun saurari rikodin din da aka dauka a lokacin da Mansur Mashi da abokan hirar sa ke babatu.

Bisa ga kalaman da Mansur ya furta, ya rika sukar salon mulkin Buhari, inda ya ce ” da Aisha ce ta samu damar da uwargidan marigayi Umaru ‘Yaradua, Turai ‘Yaradua da Najeriya ta gyaru domin za ta fi tabuka abin azo a gani fiye da yadda Buhari ke yi’

Saidai kuma jaridar Guardian ta ruwaito cewa Honarabul Mashi ya ce ba zai fadi komai a kai ba tunda ‘yan sanda na bincike akai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply