Katsina: Ku Fallasa Asirin Masu Fyade – Masari Ga Matan Katsinawa

Gwamna Aminu Bello Masari na ya yi kira ga matan jihar Katsina su rika tona asirin masu yi wa mata fyade ko kuma duka da sauran nau’in cin zarafin mata a jihar.

Ya kuma yi gargadin cewa yin shiru na nufin karfafawa masu aikata laifin gwiwa ne wurin kaucewa doka musamman wadanda suke yin sulhu da masu fyaden a biya iyayen wadanda aka yi wa fyaden kudi.

A yayin jawabin da Masari ya yi wa taron mata na kungiyar masu sanaoi, TUC, da hadin gwiwan cibiyar mata a gidan gwamnati, ya yi kira ga matan jihar su cire tsoro su rika tona asirin masu laifi domin a hukunta su.

Ya ce gwamnatin jihar ta hannun majalisar jihar ta kafa dokokin masu tsauri ga wadanda aka samu da laifin fyade ta yadda har ana iya zartar da hukuncin kisa ga masu fyaden.

“Ya ce harin ‘yan bindiga ya janyo karin samun fyade a jihar. Masu garkuwa da mutane suma su kan yi wa mata fyade ko kuma cin zarafinsu ta wasu munanan hanyoyi.

“A baya bayan nan, matasa da ke neman auren yarinya kuma aka hana su su kan hada baki da masu garkuwa da mutane domin sace amaryar domin su mata fyade.”

Ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da daukan matakan da suka dace domin magance matsalar karuwar fyade a jihar.

Shugaban cibiyar mata ta jihar, hajiya Hajara Idris ta koka game da yadda ake samun karuwar fyade a jihar a kowace rana. Ta ce an shirya taron na kara wa juna ilimi ne a jihohi 36 na kasar har da babban birnin tarayya Abuja.

Hajiya Hajara Idris ta ambata cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti na musamman domin duba matsalar cin zarafin mata musamman fyade.

Ta bukaci gwamnatin jihar ta yi koyi da abinda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ita ma ta kafa kwamiti na duba batun cin zarafin mata a jihar ta Katsina.

Labarai Makamanta

Leave a Reply