Mazauna kauyen Majifa da ‘yan banga a karamar hukumar Kankara sun kashe a kalla mutane 30 da ake zargin yan bindiga ne a jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Duk da cewa bayyanai basu kamalla fitowa ba a lokacin hada wannan rahoton, majiyarmu ta gano cewa yan kauyen sun kafa wa yan bindigan tarko ne.
Wani mazaunin kauyen ya shaidawa majiyarmu cewa lamarin ya faru ne da asubahin ranar Litinin.
“Mazauna kauyen sun samu labarin cewa yan bindigan na shirin kawo musu hari cikin dare, hakan yasa suka kafa musu tarko kuma Allah ya basu nasara suka fatattake su suka kashe a kalla 30 daga cikin yan bindigan,” in ji shi.