Katsina: Hatsarin Babur Ya Ci Ran ?an Gidan Mangal

Allah ya yi wa ?an Shahararren ?an Kasuwar nan kuma mai Kamfanin Jiragen Sama Na Max Air dake birnin Katsina, Alhaji ?ahiru Barau Mangal, wato Nura Dahiru Mangal rasuwa Sanadiyyar hatsarin da Mashin ?in nan mai gudu na tsere watau (Bike).

Alhaji Nura Dahiru Mangal ya yi hatsarin da misalin ?arfe 4:00 na Yammacin yau Laraba kusa da Kwalejin Hassan Usman Katsina.

Majiyarmu ta shaida mana cewa za’a yi jana’izarsa gobe Alhamis da Misalin Karfe 10:00 Na Safiyar Gobe A Masallacin Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, Dake Kofar Kwaya, Katsina.

Mashin ?in Bike na da matu?ar gudu sosai hakan ya sanya yake da hatsari, kuma mafi yawan ‘ya’yan masu hannu da shuni na sha’awar hawan sa, idan jama’a za su iya tunawa irin wannan Mashin ?in ne Yusuf Buhari ?an gidan Shugaban ?asa ya ta?a hatsari da shi a shekarar bara.

Related posts

Leave a Comment